Posts

Showing posts from September, 2022

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Image
  Munkaila Ahmadu,dan karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa,  ya bayyana cewa ya kashe iyayensa ne  saboda kalaman batanci da sukayi ga Annabi Muhammad (S.A.W) A cewar Munkaila, mawaki kuma dan kungiyar Tijjaniyya. 'Yan darikar iyayensa suna zaginsa suna kiransa da mahaukaci suna adawa da kasancewarsa mawakin yabon Annabi.  A ranar Alhamis ne 'yan sanda suka kama matashin Munkaila mai shekaru 37 bayan ya kashe iyayensa tare da raunata wasu mutum biyu.  Ya yi amfani da tabarya wajen kashe mahaifinsa, Ahmad Muhammad mai shekaru 70, wanda shi ne hakimin kauyen Zarada da ke gundumar Gagarawa, da mahaifiyarsa  Hauwa'u, mai shekara 60. Ahmadu, a cikin fefen Bidiyon da aka nada a hannun ‘yan sanda, ya ce bai yi nadamar abin da ya aikata ba domin an umarce shi da ya yi hakan. Sun kasance ba su kaunar Annabi Muhammadu (S.W.A). Shiyasa na kashe su, sun zagin Annabi kuma hukuncinsu kisa ne, babu tuba ga duk wanda ya zagi Annabi. Ni mawakin yabon Annabi ne, bana nayi nufin in yi vid