Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

 


Munkaila Ahmadu,dan karamar hukumar Gagarawa ta jihar Jigawa, ya bayyana cewa ya kashe iyayensa ne saboda kalaman batanci da sukayi ga Annabi Muhammad (S.A.W)


A cewar Munkaila, mawaki kuma dan kungiyar Tijjaniyya. 'Yan darikar iyayensa suna zaginsa suna kiransa da mahaukaci suna adawa da kasancewarsa mawakin yabon Annabi.


 A ranar Alhamis ne 'yan sanda suka kama matashin Munkaila mai shekaru 37 bayan ya kashe iyayensa tare da raunata wasu mutum biyu. 

Ya yi amfani da tabarya wajen kashe mahaifinsa, Ahmad Muhammad mai shekaru 70, wanda shi ne hakimin kauyen Zarada da ke gundumar Gagarawa, da mahaifiyarsa  Hauwa'u, mai shekara 60.


Ahmadu, a cikin fefen Bidiyon da aka nada a hannun ‘yan sanda, ya ce bai yi nadamar abin da ya aikata ba domin an umarce shi da ya yi hakan. Sun kasance ba su kaunar Annabi Muhammadu (S.W.A). Shiyasa na kashe su, sun zagin Annabi kuma hukuncinsu kisa ne, babu tuba ga duk wanda ya zagi Annabi.




Ni mawakin yabon Annabi ne, bana nayi nufin in yi video na waka ta kuma in sha Allahu zan yi haka, nasan za'a sakeni kuma zan samu ‘yanci domin Allah yana tare da ni, shi ya sa ban damu da halin da nake cikina a yanzu.

Ahmadu ya kuma bayyana a cikin faifan bidiyo da 'yan sanda suka dauka. Cewa , Na roƙi mahaifina ya tallafa mini aikina (waƙar yabo), kuma na gaya masa cewa ba na bin mata, ni ba ɗan caca ba ne, ba ni shan kwaya, kuma ba na yin sata, amma ya ki ya taimakamin.


Mahaifiyata ta kasance tana zuwa garuruwan da ke makwabtaka da ni domin ta bata min suna, tana ce wa mutane su ki ni duk lokacin da na zo wakar yabon Annabi saboda na haukace na ki yin aikin gona. 


Yanzu ina hannun 'yan sanda domin a tunanin mutum na yi kuskure amma a wajen Allah da Annabi abin da na yi shi ne daidai, a cewar Ahmadu.

 

Munkaila wanda ke da ‘ya’ya biyar, ya kuma ce yana zargin mahaifinsa yana lalata da matarsa.

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.