Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.
Babban hafsan sojojin Nigeria ya bayyana cewa a shirye suke da su afkawa sojojin kasar Nijer da zarar an basu izinin yin hakan.
"A shirye muke da mu afka wa sojojin Nijer da zarar an umarce mu da yin hakan. Kuma muna da tabbacin samun nasara. Ba za mu bari masu juyin mulkin su sami nasara ba. Muna da tabbacin masu juyin mulkin da magoya bayansu sun san cewa abinda suke kokarin cin mawa ba mai yuwua bane. Domin zamuyi nasara a kansu" a cewar General Christopha Musa.
Kasar Nijer dai tana fuskantar barazanar fadawa cikin yaki tsakaninta da kungiyar ECOWAS wanda kasashe goma zasu shiga tare da tallafin kasar Faransa.
Yayin da a daya gefen Nijar zata samu tallafin soji daga kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Guinea Conakry masu samun tallafin soji daga kasar Rasha.
Comments
Post a Comment