An ceto yara da almajirai ashirin da daya daga chocin ECWA inda aka maidasu kiristoci da karfin tsiya aka kuma tsaresu.
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ceto wasu yara da almajirai su ashiri da daya bayan ta kai wani samame a wani gida da ke unguwar JMDB na unguwar Tudun Wada dake garin Jos ta jihar Platue.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 13 ga watan Yuni, wani Abdul Rahman da ya gudu daga gidan ya garzaya zuwa ofishin kungiyar Jammatul Nasril Islam (JNI) don ba da rahoton cewa Cocin ECWA da ke Jos ta satosu su da karfi kuma aka maida su addinin Kiristanci.
Ya ce wasu mutane ne suka kama shi da wani Nura Usama da karfi bayan sun sa su aikin wanke musu motarsu a garin Gombe amma suka yi awon gaba da su da karfi a cikin wata mota kirar Toyota Camry, suka kai su Cocin ECWA da ke Tumfure Gombe inda suka shafe makonni uku a tsare, daga nan ne suka yi awon gaba da su. Zuwa hedikwatar ECWA da ke Jos; inda aka tantance su kuma aka kai su wani gida da ke unguwar Tudun Wada inda aka ajiyesu.
Kungiyar Jama'tul Nasrul Islam(JNI) ta kai rahoton ga jami’an DSS wadanda sukuma suka kai samame gidan tare da wanda ya gudo, Abdulrahman. inda suka ceto yara 21. Sauran yaran 19 hukumar DSS ta cigaba da aje su yayin da Abdul Rahman da Nura suka mika su ga Jama'atul Nasrul Islam.
Babban Sakataren Cocin, Rabaran Yunusa Nmadu wanda shi ma ya zanta da Aminiya ya ce ba da karfi aka kawo wadanda aka samu a gidan ba kamar yadda yaran da abin ya shafa suka yi ikirari, inda ya ce cocin ba ta mayar da kowa zuwa Kiristanci.
Ya ce gidan kamar makaranta ne da ake horar da dalibai sana’o’i daban-daban, ya kuma ce bai san wadanda suka kawo yaran gidan ba.
Sai dai yaran sun ce a karon farko da suka isa Jos a watan Oktoban shekarar da ta gabata, sun ce wa wadanda suka sato su da su mayar da su Gombe saboda iyayensu ba su san inda suke ba amma suka ki. Sun ce su Almajirai ne daga garin Azare da ke Bauchi amma suna zaune a Gombe tare da malaminsu kafin a sace su.
Comments
Post a Comment