Jam'iyyar NNPP na zawarcin Wike da wasu jiga jigan PDP domin neman lashe zaben 2023.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sen Rabi'u Musa Kwankwaso ya isa Rumuepirikom, mahaifar H.E Nyesom Ezenwo Wike.
Sen Kwankwaso wanda ya is garin da misalin karfe 7:30 na dare ya samu ganawa da wasu shugabannin jam'iyyar NNPP na jihohi. Gwamna Wike ya gana da kwankwaso ne tare da tsohon Gwamnar jihar Ekiti, Ayo Fayose da tsohon shugaban asusun kasa, AGF Bello Adoki da Cif Ferdinard Alabraba da Sanata Olaka Worgu da sauran shugabannin PDP.
Daga nan sai su biyun suka bar wakilansu domin tattaunawa ta sirri wadda ta dauki kusan awa daya ana tattaunawa. An hangi Sen Kwankwaso da tawagarsa sun bar gidan Gwamna Wike da karfe 8:40 na dare.
A kwanakin baya kadan ne dai aka ga irin wannan yunkukuri ta neman hadaka tsakanin dan takarar shugabancin kasa karkashin tutar jam'iyyar LP Labour Party, Petet Obi da sanata Rabi'u Musa Kwankwaso na Jam'iyyar NNPP.
Comments
Post a Comment