kotu ta yankewa Uwar 'yan Boko Haram hukuncin daurin shekaru Biyar a gidan yari akan damfara ta N71,400,000.

Kotu ta kama Aisha wakili wadda aka fi sani da Mama Boko Haram da laifuka biyu da suka hada da hada baki da kuma karbar kudi ta hanyar karya har naira N71,400,000 (Miliyan Saba'in da daya, Naira Dubu Dari Hudu).

A ranar Litinin 14 ga Satumba, 2020 Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Aisha Wakili da wasu mutane biyu, Tahiru Saidu Daura, Prince Lawal Shoyode a gaban mai shari'a Aisha Kumaliya na babbar kotun jihar Borno, Maiduguri.  


 A ranar Talata, 14 ga watan Yuni, 2022 Alkalin kotun Aisha Kumaliya ta yankewa Aisha Wakili, Tahiru Saidu Daura da kuma prince Lawal Shoyode hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari ba tare da zabin tara ba.  Wadanda aka yankewa hukuncin sune babban jami'in gudanarwa, manajan shirye-shirye da kuma daraktan kasa kamar yadda sunayensu yake a jere, na kungiyar Complete Care and Aid Foundation (Kungiyar mara alaka da gwamnati), NGO wadda aka ci kaddamar da ita a ranar alhamis, 27 ga watan Disamba, 2017 tare da buri da manufofi akan cibiyoyin ciyarwa Kyauta, magance  Shaye-shayen muggan kwayoyi da shaye-shayen kayan maye, sauya tunanin masu tsauraran halaye, masu karuwanci, yaki da fataucin bil'adama da kaciyar mata.

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.