kungiyar 'yan ta'ada masu radin kafa kasar Biafra zasu tallafawa 'yan kabilar Igbo don ganin su sami katin zaben Nigeria.
Kungiyar 'yan ta'adda masu nemar kafa kasar Biafra na shirye shiryen tallafawa 'yan kabilar Igbo wajen ganin sun sami katin zabe na Nigeria,
Tsohon mai taimaka wa gwamnan jihar Edo ta fanin kafar sada zumunta da sadarwa ta zamani, Jack Obinya ya walfa a shafukansa na sada zumunta inda ya rubuta cewa " kungiyar IPOB tana shirin dage dokar da ta kafa na hana fita ranar litinin a yankin kudu maso gabas damin kyale al'umar Igbo su sami karbar katinsu na zabe"
'Yan kabilar ta Igbo dai na goyon bayan dan takarar jam'iyar Labour party, Peter Obi wanda tsohon gwamnan Jihar Anambra ne kuma dan kabilar Igbo.
A cikin satin da ya wuce kafafen yada labarai sun ruwaito yadda yan kabilar Igbo mazauna Lagos ke ta fitan dango domin samun katin zabe yayinda akai ta samun rikici tsakanin su da matasan kabilar Yorbawa.
Comments
Post a Comment