Lauya ya sanya kayan bokaye zuwa kotu don nuna kalubalantarsa na baiwa yara mata damar sanya hijabi a makarantun gwamnati
Wani lauya da yayi kaurin suna wajen kalubalantar abinda wasu ke ikirari na maida najeria kasar musulunci an ganshi sanye da kayan boka yayin da ya halarci zaman kotun koli da ke Abuja ranar Alhamis.
Lauyan wanda bai sanya takalma a kafafunsa ba ya ce hukuncin da kotun koli ta yanke da ya baiwa mata 'yancin sanya hijabi a makarantu na nufin duk ‘yan Najeriya na da ‘yancin sanya suturar addininsu a ma'aikatu da makarantu.
A kwanakin bayane dai kotun koli ta yanke hukunci akan wata kara da wasu lauyoyi musulmai suka daukaka suna neman tabbatar da 'yancin addini/sanya hijabi ga mata musulmai a makarantu. Bayan wani rikici da ya barke a wani yanki na jihar kwara sakamakon han yara dalibai mata sanya hijabi a wata makarantar gwamnati, lamarin fa ya janyo rasa ran wani matashi musulmi yayin zanga zangar nemar wa dalibai mata 'yancin sanya hijabi.
Da yake magana da ‘yan jaridan, ya ce,
“ a bisa hukuncin da kotun koli ta yanke, an ba mu lasisin yin shigar kaya irin ta addininmu. Zai zama babban take hakkina na ‘yancin saka sutura da lamirin addini idan har wani yayi yunkurin hana ni.”
Lauyan dai yayi kaurin suna wajen kaluba lantar shiri da wasu ke zargi na maida Najeria kasar musulunci. Shine wanda ya shigar da kara a kotu domin ganin an goge rubutun ajami dake kan takardun Naira.
Comments
Post a Comment