Shugaban yan bindiga ya gargadi mutane da kar su zabi jam'iyyar APC a zabe mai zuwa.

Ana iya jin muryar shugaban ‘yan bindigar a cikin wani faifan sauti da aka nada daga wata wayar tarho da suka yi tsakaninsa da shugaban wata kungiyar masu siyar da kayan waya daga Zamfara a lokacin da suke ciniki a kan kudin fansa domin a sako mambobin kungiyar da yawansu ya kai ashirin da tara wanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.  

 Shugaban ‘yan bindigar ya bukaci al’ummar garin Zamfar da su zabi sanata Kabiru Marafa, saboda sun amince cewa zai iya kawo karshen matsalar tsaro a jihar.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa game da sauya shekar da Gwamna mai ci Bello Muhammad Matawalle yayi zuwa jam'iyar APC a matsayin nakasa harkar siyasar sa.

Muryar wanda shugaban ‘yan kasuwar ya nada mai suna Vice(lakabi) ya dauki tsawon mintuna goma. yayin cinikin fansa na ganin an sako matasan ‘yan kasuwa ishirin da tara.

 ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dubban mutane a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da kuma Kaduna da ke yankin Arewa maso yammacin Najeriya inda daga cikin dukkan jihohi shida na yankin jam’iyyar adawa na mulkin a Sakkwato ne kawai.

 Saurari sauti: https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=5277551318955168&id=100001010576116

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.