Dauka aikin 'dan-sanda - Abubuwan da kake bukata domin zama 'dan-sandan Nigeria.

Rundunar 'yansandar Nigeria na gab da fara dibar ma'aikata na ahekarar bana na masu matsayin kurtu(constables).
Masu sha'awa ko neman zama 'Dan-sanda su sani cewa zasu iya cika fam din neman chanchanta ne kadai a shafin da hukumar ko rundunar 'yansanda ta kasa zata fitar.

 Rundunar ‘yan sandan Najeriya (NPF) ta bayyana karara a Shafinta na yanar gizo www.npf.gov.ng cewa daukar ma’aikata a hukumar babu wata kumbiya-kumbiya a ciki kuma kyauta ne cika fam din nema.  Wanda hakan yana nufin cewa muddin kuna da takaddu da yanayin da ake buĆ™ata, kaima ka cancanci shiga sahun wanda zasu nema kuma a dauke su a matsayin jami'an 'yan sanda.

Bukatun da aka nema a daukar da akayi na baya bayan nan.

Shekaru mafi karanci -         -   17

Shekaru mafi girma              -   25

Mafi tsawo da ake bukata   -   1.67

Mafi gajarta da ake bukata -   1.64

Takardun karatu: sun hada da CREDIT biyar a WASSCE ko NECO wanda suka hada lallai da lissafi(Math) da kuma Turanci(English).

Karin wasu takardu kamar digiri, difloma na kowani fannin ilimi da kuma sanin computer. Zai kara gimama damar daukar aiki ga mai sha'awar zama 'dansanda.

Ku cigaba da bibiyar shafin mu domin kawo muku sabon labari game da daukar ma'aikata. Kuma zaku iya tofa albarkacin bakin ku a kasan labarin nan.

Yada wanan don ilmantar da wasu suma.

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.