kungiyar kiristicin Arewa taje fadar shugaban kasa kuma tayi barazanar daukar mataki abisa cin mutuncita na daukar musulmi a matsayin mataimaki shugaban kasa.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu Kiristoci sukayi takanas ta kano cikin motocin safa daga jihohin Arewa 19 suka inda suka taru a Abuja domin nuna rashin amincewarsu da takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar APC, wanda Asiwaju Bola Tinubu, ya zabi Musulmi a matsayin mataimakinsaq.

 Masu zanga-zangar sun yi tattaki zuwa fadar shugaban kasa domin gabatar da takardar zanga-zangar a yayin da suke kururuwar wakokin hadin kai karkashin tutar daukacin al’ummar Kiristocin Arewacin Najeriya.

 Labarin ya zo ne kwanaki biyu bayan da wasu gungun matasan Kiristocin Arewa suka gudanar da zanga-zangar nuna adawa da zaben tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai Musulmi da Musulmi a babban zaben 2023.

 Kungiyar wacce ta kunshi matasa Kiristocin APC daga jihohin Arewa 19, ta yi rantsuwar cewa mambobinta ba za su yi wa jam'iyyar yakin neman zabe ba.

 Yayin da yake ikirarin cewa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya ci amanar ‘yan Najeriya inda ya zabi Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa.  Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin cin mutunci ga Kiristocin Arewa.

 Moses Adams wanda shi ne ya shirya zanga-zangar arewa, ya zanta da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda  ake nuna wa kiristoci saniyar ware.

 Kamar yadda ka sani, Najeriya kasa ce mai kabilu da addinai daban-daban.  Musulunci da Kiristanci sune manyan addinai a cikin al'umma.  Kuma tun lokacin da al’ummar kasa suka sami ‘yancin kai a shekarar 1960,  salon rayuwarmu ya nuna kokarin mu na tabbatar da daidaito a shugabancin al'umma, gwamnatocin da suka shude a kasar sun amince da tsarin addinai daban-daban na al'ummar kasar, musamman a lokacin zabe.  Don haka, mun ga abin mamaki ne yadda jam’iyyar APC ta zabi dan takararta na mataimakin shugaban kasa a zaben 2023 ba tare da yin la’akari da al’ummar Kirista ba.  Babu shakka, wannan ba abin amincewa ba ne kuma hanya ce ta haifar da baraka tsakanin Musulmi da Kiristan Nigeria.

 Musa ya yyli anfani da damar ya mika wasikar zanga-zangar da kungiyarsa ta aika wa shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya).

 Ya yi ikirarin cewa zabin da Tinubu ya yi na zabar Shettima a matsayin mataimaki bai dace da ra'ayin al’ummar kasa ba a wannan lokaci mai muhimmanci a tarihin kasarmu.

 Wani bangare na wasikar ta ce, "Mai girma shugaban kasa, tun lokacin da aka dawo da mulkin dimokuradiyya a Najeriya a shekarar 1999, al'ada ce ga dukkan jam'iyyun siyasa su hada Musulmi da Kirista ko Kirista da Musulmi."  Kuma hakan ya taimaka matuka wajen wanzar da hadin kan addinai a cikin al'umma.

 To sai dai matakin da jam’iyyarmu ta dauka na goyon bayan tikitin tsayawa takara tsakanin musulmi da musulmi, shi ne kololuwar kiyayyar da aka nuna wa kiristoci a cikin al’ummarmu da kuma rashin mutuntawa matuka.  Ya ci gaba da cewa hakan na zuwa ne bayan da wasu kungiyoyin shugabannin jam’iyyun siyasa suka kiyaye tare da la'akari da addinai kamin suyi nasu zabin.

 Mu Kiristocin Arewacin Najeriya, mun ji takaici, mun kuma fusata da wannan rashin adalci, ya mai girma shugaban kasa.  Abubuwan da APC ta yi na nuna cewa Kiristoci ba su da anfanin komai a cikin babban al’ummarmu.  Jam’iyyar APC ta kuma nuna rashin mutunta addini, wanda idan ba a yi maganinsa ba a kokarin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, to a karshe zai haifar da rikicin addini a cikin al’umma.

 Muna amfani da wannan kafar domin yin kira ga ofishinka mai girma da ka sa baki wajen ganin an soke wanan zabi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya yi.  “A matsayinmu na masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, mun san cewa akwai kiristoci masu kishin kasa a jam’iyyar APC daga Arewacin Najeriya da sauran sassan kasar nan wadanda suka sadaukar da kai kuma suna da kwazon da suka cancanta abasu damar tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa, muna bukatar ka gaggauta umurtar dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar da ya gaggauta sauya matakin nasa na daukar musulmi.

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.