Munafurcin siyasa da yunkurin karya Arewar da ta yi watsi da tarihi. daga rubutun Sheikh Gumi.


Daga cikin wani rubutu da Sheik Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya wallafa a shafukansa na zumunta. ya fara da karin magana na wani fitaccen bature mai suna, Robert A. Heinlein, inda yake cewa "duk wani tsarin rayuwa da yayi watsi da tarihi zai sa a rasa fahumtar yadda ake ciki a rayuwa dakuma inda rayuwar ta dosa
 
Sheikh Gumi ya tuna wa 'yan arewa da  ranar 15 ga watan Janairun 1966,  wanda a ranar ne Manjo Chukwuma Kaduna Nzeogwu, wanda ya kasance hafsan Sojojin Nijeriya ne dan kabilar Ibo. ya jagoranci kashe Ahmadu Ibrahim Bello, Sardaunan Sakkwato, ba tare da wani dalili da ya wuce na kabilanci bangaranci. Wanda hakan ya janyo Arewa ta rasa babban jigo a siyasa.  A wannan rana kuma an kashe firayim minista, Abubakar Tafawa Balewa wanda shima ya rasa ransa a hanun sojojin.  
Kisan nasa ya sa Al'ummar Nigeria da musamman Arewa sunyi hasarar shugaba mafi ƙwazo a tarihin Nigeria sakamakon kabilanci.

Ya ci gaba a rubutun da cewa "Duk da kisan da aka yi wa shuwagabanin arewa a yanayi na juyin mulki, yankin kudu maso yamma da kudu maso gabas basu rasa nasu shugabanin ba wanda suma suna cikin gwamnati. sun sami nasarar adana shugabannin siyasar su wanda hakan ya basu damar kwarewa a kan makircin siyasa na gwagwarmayar neman mulki. Yayinda sukuma 'yan Arewa suka rasa masu kare muradunsu a siyasar Nigeria"
 
Ya kuma tunatar da 'yan Arewa rana da kuma yada aka kashe Janar Murtala da kuma wanda ya kashe shi.
Inda ya ce "bayan shekaru goma a ranar 13 ga watan Fabrairun 1976, Janar Murtala Ramat Muhammed shi ma aka sami wani Laftanal Kanal Buka Suka Dimka, wani dan kabilar Langtang, kuma shima kirista kamar Nzegu Kaduna ya kase shi har lahira.  Murtala dan kishin kasa ne wanda ke auren wata daga kabilar Yarbawa.  Don haka abin da ya fito fili ya kashe shi da dan uwansa Dan Arewa ya yi ba don komai bane sai don banbancin addini."

A rubutun na sa ya fadi dalilan da suka sa har yanzu shuwagabani daga Arewa basu iya mulki cikin jin dadi ko natsuwa ba inda ya bayyana su da cewa 
"kisan gilla da aka yi wa wadannan manyan jagororin Arewa, yankin ya zama koma baya a siyasa ta bangaren kare muradin Arewa a siyasance. A bisa wanan daliline siyasar Arewa take a gurgunce a karkashi manyan 'yan siyasu na kudu. yankin, Arewa kuma na ci gaba da gwagwarmayar samun wuri a mulki",

 ''Tashe-tashen hankula da sace-sacen da suka addabi yankin Arewa a yau, bai rasa nasaba da wannan tabarbarewar harkokin siyasa ba. domin kuwa Arewa a wargaje take ba tare da ta gaji wani abu na siyasa ba a daga wajen ainihin iyayenta na farko ba kamar tarbiya ta biyayya da mutunta juna".

Ya kuma bayyan cewa mafiya yawan jagorori 'yan Arewa basu kishin yanki da jama'ar ta. 
"A yanzu wasu kadan ne masu fada a ji dake ke magana cikin damuwa da yankin na Arewa, amma yawancin shugabannin siyasar Arewa a yanzu abinda suke yi bai wuce biyan bukatun kansu ba da kare muradun su na siyasa, kuma hakan ke bayyana dalilin da ya sa yankin ya shiga cikin wani hali na tabarbarewar tattalin arziki da tsaro". 

A cikin rubutun nasa ya zaburar da musulmai yan Arewa da su fahimci irin kokari da akeyi na karya siyasar su da bautar da su a siyasance. Inda ya kwatanta da cewa 
"Ka yi tunanin inda a ce yankin kudu maso gabas ne ko kudu maso yamma aka samu wani soja dan Arewa ya kashe wani daga cikin shugabanninsu na yankin ko kuma su ke da yawan al'umma fiye da Arewa, wane irin adalci za suyi mana a lokacin",
"Jamhuriyar Kamaru da jamhuriyar Benin makwabtan mu ne da zamu iya daukar aya daga garesu,
Kuma duk mai hankali ya fahimci me hakan yake nufi".

Ya kuma koka da yanda Arewa ta zama wata garkuwa ga kasancewar Nigeria kasa daya wanda duk da hakan bai anfane ta ba. Inda yake cewa 
''duk da yunkurin kashe Arewa da a kayi tayi, Arewa ta ci gaba da zama mai kokarin hada kan 'yan Nigeria am matsayin Al'umma daya. Sai dai a yanayi na makirce-makircen siyasa babu wani dan Arewa da zai tsaya domin kare muradu da mutuncin Arewa.  Musamman irin yadda ake kashe 'yan Arewa kuma ake kone motocinsu da kayan kasuwancinsu da kuma wa'anda ake kashe dabbobin su. Sannan har akwai lokacin da aka taba bukatan yan Arewa dake wani yanki a kudu su rataya shaida ko tambari domin a rinka tantancesu duk inda suke"

Ya kuma bayyana Arewa a matsayin yankin da zai ceci Nigeria daga rugujewa ta hanyar samar da shugaba da kishin kasa.  
''Shugaba mai kishin kasa kamar Janar Murtala ne kadai zai iya hada kan al’ummar kasar waje daya. Shugaba da bashi da kabilanci a ransa. Wanda ya yi imani da Nijeriya a matsayin kasa daya a zuciyarsa, ba don manufar siyasa ko boyayyar manufa ba''.

A karshe yayi fata da addu'ar Allah ya warwarewa Nigeria matsalolinda suka mamayeta kuma ya daukaketa.

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.