NNPC bazata sake zuba kudi a asusun raba kudin kasa ba bayan mika kamfanin ga hanun yan kasuwa.

Bayan bayyanar da mika ragamar kamfanin tonon manfetur na Nigeria ga hannun 'yan kasuwa da gwamnati tarayya tayi lamarin ya cigaba da daukar hankalin mutanen Nigeria.

Hakan dai na faruwa ne tun bayan lokacin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kaddamar da kamfanin mai na NNPC Limited a ranar Talatar da ta gabata, ya kuma bayyana cewa daga yanzu sabuwar kamfanin ta fita daga ka’idojin gudanarwa na gwamnati.

Shugaba Buhari, kuma ya bayyana a fadar shugaban kasa dake Abuja, cewa daga yanzu kamfanin mai na kasa zai ci gaba da gudanar da aikinsa a karkashin kyakkyawan tsarin kasuwanci na duniya. Kamar sauran takwarorinsa, Armaco na Saudiyya da kuma Petrobras na kasar Brazil.

Wannan rahoton zai bayyana muku yadda sabon tsarin kasuwanci na kamfanin manfetur na kasa zai gudana
Daga cikin bayanai dake kunshe a cikin  Dokar Masana'antar Man Fetur(petroleum industrial act) a turance, wanda ya fahimtar da 'yan kasa yadda sabon tsarin kasuwancin na yanzu zai gudana. 
Tsarin ya nuna cewa daga yanzu gwamnati bazata sake sanya, NNPC ba a cikin jerin hajojinta na kasuwar hada-hadar hajoji ta kasa wato(Nigerian stock Exchange) a turance.
Kamfanin a yanzu zai zama kamfani mai zaman kansa tare da rigistar mallaka mai kason hanun jari gida biyu 50:50 ga Ma'aikatar Man Fetur ( Ministry of Petroleum Incorporated) da Ma'aikatar Kuɗi (Ministry of Finance Incorporated). Wanda haka ya sa ma'aikatar ta zama kamfani mai zaman kanta na gwamnati gabaɗaya (mai juya jari don samar da riba).  

Kamar yadda shugaban kamfanin NNPC Limited, Mele Kyari, ya bayyana cewa baza su sake zuba kudi a asusun kwamitin rarraba kudin kasa ba(FAAC). sai dai zasu biya gwamnati haraji da kudin karrama masu ma'adinai sannan kuma zasu raba riba tsakaninsu da masu hanun jari wato Ministry of Petroleum Incorporated da Ma'aikatar Kuɗi Ministry of Finance Incorporated wanda sukuma suna zuba ribar da suka samu a asusun hukumar Rarraba kudi ta kasa FAAC. 

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.