Tallfi da farashin mai - Shin ko kasan cewa 'Yan Nigeria zasu sayi man fetur sama da Naira dari biyar zuwa dari bakwai?

Tallafin man fetur a Najeriya yana lakume kudade masu yawa daga asusun gwamnati.  A kiyasi na baya baya nan, gwamnati ta ba da tallafin man fetur da kudin sa yakai dala biliyan $3.9b - kusan ninki biyu na kasafin kudin da gwamnati ke ware ma kiwon lafiya. tallafin yazama dole ne  saboda gwamnati ta kayyade farashin man fetur kasa da farashinsa a kasuwar duniya kuma tana amfani da kudaden asusunta don biyan cikon kudin a farashin duniya.  An fara saka tallafin mai a Najeriya ne a cikin shekarun 1970 a matsayin matakin saukakawa al'umma sakamakon tashin farashin mai a kasuwar duniya a shekarar 1973. Sai dai duk da yunƙurin kawo daidaita al'amuran, Nijeriya ba ta taɓa samun nasarar cire tallafin man fetur ba, sakamakon tsananin adawar da jama'a ke yi na kawo gyara da zai kaiga cire tallafin.  Irin wannan tallafin yana da illoli masu yawa ga tattalin arziki da ke hana yin anfani da kudaden wajen aiwatar da manufofin ci gaba;  yana rage yawan kaso na rabon albarkatun kasa ga gwamnatocin jihohi;  akasarin tallafin ya fi kyautatawa talakawa ‘yan Najeriya ne;  kuma samar da mai da arha yana kawo, cunkoso ababen hawa da sauyin yanayi.  Duk da haka, bincike ya nuna cewa kashi 70% cikin 100% na ‘yan Najeriya na adawa da rage ko cire tallafin. 
Kamin karin farashin ko rage tallafin mai da gwamnati ta yi a farkon satin da muke ciki. ya kasance gwamnati na biyan tallafi ga duk wanda ya sha mai da ya kai Naira dari hudu da ashirin da daya 421 a kowace lita guda. Rage tallafin ko karin farashi da gwamnati tayi a yanzu ya ban banta tsakanin yankunan siyasa shida da najeria take da su. Sabon farashin ya tashi daga Naira zuwa 165-173 zuwa 169-189.
Jerin sabon farashi a yankunan guda shida.
1. Kudu maso yamma - N179
2.Arewa maso yamma- N184
3.Arewa maso gabas  - N189
4.kudu maso kudu       - N179
5.Arewa maso tsakia  - N179
6.kudu maso gabas    - N184

Sai manyan biranen;
Lagos   - N169
Abuja   - N174

Duk sanda Gwamnati ta cire tallafin da take baiwa man fetur baki daya. 'Yan Nigeria zasu sayi mai a farashin sama da Naira dari biyar N594.07 zuwa dari bakuwai N700

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.