El-rufa'i zai zama minista a karo na biyu bayan mika sunansa da Tinubu yayi ga majalisar tarayya.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen mutane 28 na sunayen ministoci ga majalisar dattawa a hukumance. Jerin sunayen na
kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar a jiya, Alhamis, 27 ga watan Yuli,
2023.
Shugaban ma'aikatar fadar gwamnati Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai, ne ya gabatar da jerin sunayen ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio a daidai karfe
01: 19pm.
Wadanda ke cikin jerin sunayen sun hada da: Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, da takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, da kuma
fitaccen malami kiwon lafiya, Ali Pate. Har ila yau, wadanda Tinubu ya zaba a matsayin ministocin sun hada da babban lauya Lateef Fagbemi (SAN); da wani masanin tattalin arziki Olawale Edun, sai ma'aikacin banki Adebayo Adelabu, da
tsohon gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi,
shugabar mata ta jam'iyyar APC Misis Betta Edu,
Sanata Ben Ayade na jihar cross Ribas da fitacciyar 'yar jarida Dele
Alake, wacce a halin yanzu ita ce mai ba da shawara ta musamman kan harkokin yada labarai ga shugaba Tinubu.
Ga cikaken jerin sunayen a kasa:
1. Abubakar Momoh
2. Ambassador Yusuf Miatama Tukur CON
3. Arch. Ahmed Dangiwa
4. Barr. Hannatu Musawa
5. Chief Uche Nnaji
6. Dr. Berta Edu
7. Dr. Dorris Aniche Uzoka
8. H.E. David Umahi
9. H.E. Nyesom Wike
10. H.E. Badaru Abubakar CON
11. H.E. Nasiru Ahmed Elrufai
12. Rt. Hon. Ekperipe Ekpo
13. Hon. Nkiru Onyeojiocha
14. Hon. Olubunmi Tunji Ojo
15. Hon. Stella Okotette
16. Hon. Uju Kennedy Ohaneye
17. Mr. Bello Muhammad G.
18. Mr. Dele Alake
19. Mr. Lateef Fagbemi SAN
20. Mr. Muhammad Idris
21. Mr. Olawale Edun
22. Mr. Waheed Adebayo Adelabu
23. Mrs Iman Suleiman Ibrahim
24. Professor Ali Pate
25. Professor Joseph
26. Senator Abubakar Kyari
27. Senator John Eno
28. Senator Sani Abubakar Danladi
Comments
Post a Comment