Nijar ta dakatar da sayarwa kasar Faransa gwal da makamashin Uranium kuma ta nuna ma Amurka da ECOWAS yatsa.
Sabon shugaban kasa na soji a Nijer Gen. Abdourahamane Tchiani ya bayyana dakatar da sayarwa kasar Faransa da zinari da kuma makamaahun Uranium.
Kaso mai girma na wutar lantarki da ake amfani dashi a Faransa ana samar da shine daga makamahin Uranium. Inda kididdiga ya nuna cewa a kowani daya 1 cikin uku 3 na kwan lantarki a Faransa yana amfani ne da makamashin Uranium da ake samowa daga Nijer. Amma duk da haka kaso 18% ne kacal cikin dari 100% na yan kasar Nijer ke iya ganin wutar lantarki a kasarsu.
Itama kasar Amurka ta sanar da janye tallafi da take baiwa kasar na Nijer. Yayinda sabon Jagoran soji na Nijer Gen. Abdourahamane Tchiani ya mayar da martani da kira ga Amurka da ta rike tallafin nata domin tafi Nijer bukatar su domin tallafawa miliyoyin yan kasar ta da basu da wurin kwana suke rayuwa a titi. Ya kara da cewa duk mai baka riga ka dubi ta wuyarsa.
Ya kuma gargadi kungiyar ECOWAS ga duk wani yunkuri na amfanu da karfin soji wajen tsoma baki a cikin lamarin na kasar Nijer.
ECOWAS dai ta lakabawa Nijer da sjojinta takunkumi tare da bada wa'adin sati daya a maida mulki ga Bazoum ko ta dauki matakin soji akan sojojin na Nijer.
Mutanen kasa ta Nijer suna cigaba da zangazangar nuna goyon bayan sojojin kasar inda suke ta daga tutar kasar ta Nijer da na Rasha.
Comments
Post a Comment