Taron Rasha-Afirka: Rasha zata bai wa kasashen Afirka alkama kyauta domin maganin tsadar abinci.

A lokacin taron da aka lakabawa suna Taron Rasha da Afirka. Wanda ya sami halarcin shuwagabannin kasashen Afirka sama da ashirin da kuma wakilai daga sauran kasashe sama da ashirin. Shugaba putin na kasar Rasha ya bayyana cewa zasu samar wa  kasahen Afirka da hatsi kyauta.
"A shirye muke da mu fara baiwa kasashen Burkina Faso, Zimbabwe, Mali, Somalia, Afirka ta tsakia da Eritrea hatsi mai nauyin tonne dubu ashirin da biyar zuwa hamsin 25-50,000 kyauta daganan zuwa watanni uku," a cewar Putin.

Ya kara da cewa, kasarsa Rasha tana shiryawa domin maye gurbin Ukrain wajen samar wa Afirka da hatsi(alkama) a dukkan bangarorin kasuwanci da tallafi. Domin cimma manufar da Rasha ta kira samar da abinci ga duniya baki daya.
Kasar ta Rasha ta watsar da wata yarjejeniyar da aka kulla domin amincewa ga Ukrain ta cigaba da fitar da hatsi(alkama) zuwa ga kasashen duniya duk da yaki dake tsakanin kasashen biyu.

Bayan wargajewar yarjejeniyar, kasar Rasha ta soma kai hare-haren bamabamai a tashar jirgin ruwa dake kogin Danube wanda kasar Ukrain take amfanu dashi wajen fitar da ababen da take sayarwa a waje. Hakan shi ya sanya aka sami tashin gouron zabi na alkama a kasuwan duniya baki daya a cikin kwanaki Goma da suka shige.

Putin ya bayyana dalilan da suka sa yarjejeniyar ta wargaje da cewa sama da kashi 70% na alakamar da Ukrain take fitarwa a karkashin yarjejeniyar tana sayar da sune ga kasashe masu arziki. Yayin da kasashe matalauta kamar Sudan ke samun damar siyan kashi 3% kacal kasa da abinda take bukata. Duk da sonkai da Ukrain take yi wajen sayar da alkamar farashi ya cigaba da zama mai rangwame. Amma sai dai Putin bai amince da cutar da Afirkan ba waje nuna son kai da Ukrain take yi wajen sayar da alkamar.

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.