Amurka na zargin China zata iya juya akalar gwamnatin Najeriya yanda take so ta hanyar bata basussuka.
Kasar Amurka ta bayyana wa duniya cewa kasar China na yunkurin saye Najeriya ta hanyar bata basussuka wanda za bata damar juya akalar gwamnatin Najeriya.
Amurkan ta bayyana zargin da take ne a dai-dai lokacin da take matsa lamba ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu domin ganin ya dauki matakai masu tsauri akan shuwagabannin mulkin soji na Nijar wanda zai hada da afkawa kasar ta Nijar da yaki.
Wani masanin harkokin difulomasiyar duniya ya bayyana cewa zargin na amurka bai rasa nasaba da yunkuri na tilastawa Najeriya aiwatar da abinda kasashen yamma ke bukatar Najeriya tayi mata game da kasar Nijar. Ta hanyar bakanta Najeriya da alakanta ta da gwamnatin China mai mulkin gurguzu.
Kasar China dai ta zuba hannayen jari na biliyoyin daloli a Najeriya tare da baiwa Najeriyar basussuka masu yawa gwamnatin Najeriya take amfani dasu domin aywatar da ayyukan cigaba cikin gaugawa. Wanda suka shafi manyan ayyuka na habaka sufuri da masana'antu.
Comments
Post a Comment