zamu yaki kungiyar ECOWAS muddin tayi amfani da karfin soji a Nijer cewar kasahen Mali, Burkina Faso da Guinea Conakry.

Kasashen Burkina faso, Guinea Conakry da jamhuuriyar Mali
Sun gargadi kungiyar kasashen Afirka ta yamma ECOWAS cewa bazasu lamunci duk wani matakin soji a kan kasar Nijar ba.

Shuwagabanin kasashen na Burkina Faso da Mali da Guinea sun bayyana matsayarsu ne game da hukuncin da kungiyar ECOWAS ta yanke bayan kammala taron ta na gaggawa da ya gudana a ranar 30 ga Yuli, 2023 a Abuja. Game da juyin mulki a Nijar.

Matsayar da kasashen uku suka fitar na hadin guwiwa wanda ya samu sa hannun kasashen Burkina Faso da Mali, sune kamar haka:
1. Bayyana goyon bayan al'umar kasashensu na Burkina Faso da Mali da Guinea ga 'yan uwansu na Nijer wadanda suma suka yanke shawarar daukar kawar da mulkin mallaka da ke cigaba da dabaibaye kasarsu,

2. Sun kuma yi Allah wadai da matakin kungiyoyin ECOWAS da UEMOA na yankin Afirka ta yamma a bisa kakaba takunkumi wanda ke kara tsananta wa al'umma da kuma kawo cikas ga karfafa kishin Afirka a yankin na yammacin Afirka.

3. Sun kuma nuna kin amincewarsu ga bada goyon baya da aiwatar da wadannan haramtattun takunkuman wadanda suka saba doka tare da tauye hakkin bil'adama a kan jama'a da hukumomin Nijar;

4. Sun yi gargadin cewa duk wani matakin soji a kan kasar ta Nijar zai zama ayyana yaki ne da kasashen na Burkina Faso da Mali;

5. Sun kuma yi gargadin cewa duk wani matakin soji a kan Nijar zai haifar da ficewar kasashen na Burkina Faso da Mali daga cikin kungiyar ECOWAS, tare da daukar matakan kare kai na tallafawa sojojin kasar da al'ummar Nijar;

6. Sai gargadi game da mummuna sakamakon da zai biyo bayan duk wani daukar mataki na soji a Nijar wanda ka iya kawo tabarbarewar tsaro da zaman lafiya a yankin baki daya kamar yadda tsoma bakin kungiyar tsaro ta NATO bai haifar da alkhairi ba ga kasar Libya wanda shi ne tushen fadada ayyukan ta'addanci a yankin Sahel da yammacin AFRICA. Shuwagabannin soji na Burkina Faso da Mali sun fusata matuka da kuma mamakin rashin adalci na kungiyoyin.

Comments

Popular posts from this blog

YANKAN KAI- matashi ya yanke kan dansa domin neman kudi.

Banyi nadamar kashe iyayena ba domin na kashesune sabida kaunar manzon Allah a cewar mawakin tijjaniyyah

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.