Posts

Showing posts from July, 2023

Nijar ta dakatar da sayarwa kasar Faransa gwal da makamashin Uranium kuma ta nuna ma Amurka da ECOWAS yatsa.

Image
Sabon shugaban kasa na soji a Nijer  Gen. Abdourahamane Tchiani ya bayyana dakatar da sayarwa kasar Faransa da zinari da kuma makamaahun Uranium.  Hakan na zama martanine bayan kasar Faransar ta dakatar da tallafi da take baiwa kasar ta Nijer. Kaso mai girma na wutar lantarki da ake amfani dashi a Faransa ana samar da shine daga makamahin Uranium. Inda kididdiga ya nuna cewa a kowani daya 1 cikin uku 3 na kwan lantarki a Faransa yana amfani ne da makamashin Uranium da ake samowa daga Nijer. Amma duk da haka kaso 18% ne kacal cikin dari 100% na yan kasar Nijer ke iya ganin wutar lantarki a kasarsu.  Itama kasar Amurka ta sanar da janye tallafi da take baiwa kasar na Nijer. Yayinda sabon Jagoran soji na Nijer Gen. Abdourahamane Tchiani ya mayar da martani da kira ga Amurka da ta rike tallafin nata domin tafi Nijer bukatar su domin tallafawa miliyoyin yan kasar ta da basu da wurin kwana suke rayuwa a titi. Ya kara da cewa duk mai baka riga ka dubi ta wuyarsa. Ya kuma gargadi k

Shahararren mawaki dan kasar Amurka mai hannaye hudu ya bayyana.

Image
Shahraren mawakin gambara na kasar amurka mai suna Daylyt ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya nuna hotunansa tare da bayyana cewa maganar boye-boye ta kare yanzu kam zai bayyanawa duniya irin halittar da Allah yamasa. "Allah bai hallici dukkan dan adam dai-dai da juna ba! Yanzu na fahimci dukkan mutane ba daya suke ba. Yanzu na fahimci abinda aka jarabceni da shi alkhari ne ga rayuwa ta! Yanzu kam bana tsoro ko jin kunyar bayyana yadda Allah ya halicceni! Allah yace ma dan adam kazo duniya yadda nayika batare da ka biyani sisin kobo ba! Dalilin haka yasa nima ganinan nazo cikin aminci. Wannan dai bai kasance sabon abu ba domin aduniya Allah ya kanyi halittu iri daban-daban, har da mutanema sukan bambanta a halittar su.

Taron Rasha-Afirka: Rasha zata bai wa kasashen Afirka alkama kyauta domin maganin tsadar abinci.

Image
A lokacin taron da aka lakabawa suna Taron Rasha da Afirka. Wanda ya sami halarcin shuwagabannin kasashen Afirka sama da ashirin da kuma wakilai daga sauran kasashe sama da ashirin. Shugaba putin na kasar Rasha ya bayyana cewa zasu samar wa  kasahen Afirka da hatsi kyauta. "A shirye muke da mu fara baiwa kasashen Burkina Faso, Zimbabwe, Mali, Somalia, Afirka ta tsakia da Eritrea hatsi mai nauyin tonne dubu ashirin da biyar zuwa hamsin 25-50,000 kyauta daganan zuwa watanni uku," a cewar Putin. Ya kara da cewa, kasarsa Rasha tana shiryawa domin maye gurbin Ukrain wajen samar wa Afirka da hatsi(alkama) a dukkan bangarorin kasuwanci da tallafi. Domin cimma manufar da Rasha ta kira samar da abinci ga duniya baki daya. Kasar ta Rasha ta watsar da wata yarjejeniyar da aka kulla domin amincewa ga Ukrain ta cigaba da fitar da hatsi(alkama) zuwa ga kasashen duniya duk da yaki dake tsakanin kasashen biyu. Bayan wargajewar yarjejeniyar, kasar Rasha ta soma kai har

El-rufa'i zai zama minista a karo na biyu bayan mika sunansa da Tinubu yayi ga majalisar tarayya.

Image
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunayen mutane 28 na sunayen ministoci ga majalisar dattawa a hukumance. Jerin sunayen na kunshe ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisar a jiya, Alhamis, 27 ga watan Yuli, 2023.  Shugaban ma'aikatar fadar gwamnati Femi Gbajabiamila, tsohon kakakin majalisar wakilai, ne ya gabatar da jerin sunayen ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio a daidai karfe 01: 19pm. Wadanda ke cikin jerin sunayen sun hada da: Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, da takwaransa na jihar Ribas, Nyesom Wike, da kuma fitaccen malami kiwon lafiya, Ali Pate. Har ila yau, wadanda Tinubu ya zaba a matsayin ministocin sun hada da babban lauya Lateef Fagbemi (SAN); da wani masanin tattalin arziki Olawale Edun, sai ma'aikacin banki Adebayo Adelabu, da tsohon gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi, shugabar mata ta jam'iyyar APC Misis Betta Edu, Sanata Ben Ayade na jihar cross Ribas da fit