Posts

Yayinda 'yan Kannywood suka gaza. Ahmed Musa siya wa Karkuzu gida na miliyan biyar da rabi.

Image
Shararren dan wasan kwallon kafa na super eagle na Nigeria Ahmed Musa ya cika alkawarin da yayi wa shahararren dan wasan fina-finan Hausa Karkuzu. Inda yayi masa alkawarin gida da kuma kudi naira dubu dari biyar. Super Eagles Captain Ahmed Musa has redeem his pledge of 5.5 million naira house in Jos and 500,000 naira cash to the veteran kannywood actor Abdullahi Shuaibu popularly known as Baba Karkuzu.  Jagoran yan wasan kwallon kafa na Najerian Ahmed Musa ya cikia alkawarin ne ga tshohon Jarymin na kannywood Abdullahi Shu'aibu wanda akafi sani da karkuzu inda ya saya masa gida na miliyan biyar da rabi 5.5 million a cikin garin Jos tare da bashi tsabar kudi naira dubu dari biyar 500,000. Idan baku manta ba Amed Musa yayi wa baba Karkuzu alkawari ne bayan bayyanan fefen bidiyo da aka yada a kafafen sada zumunta inda akaga Karkuzun yana neman taimako na samun gidan zama. May Allah reward Ahmed Musa MON and bless his wealth. Wanna dai ba shine karon

Amurka na zargin China zata iya juya akalar gwamnatin Najeriya yanda take so ta hanyar bata basussuka.

Image
Kasar Amurka ta bayyana wa duniya cewa kasar China na yunkurin saye Najeriya ta hanyar bata basussuka wanda za bata damar juya akalar gwamnatin Najeriya. Amurkan ta bayyana zargin da take ne a dai-dai lokacin da take matsa lamba ga shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu domin ganin ya dauki matakai masu tsauri akan shuwagabannin mulkin soji na Nijar wanda zai hada da afkawa kasar ta Nijar da yaki. Wani masanin harkokin difulomasiyar duniya ya bayyana cewa zargin na amurka bai rasa nasaba da yunkuri na tilastawa Najeriya aiwatar da abinda kasashen yamma ke bukatar Najeriya tayi mata game da kasar Nijar. Ta hanyar bakanta Najeriya da alakanta ta da gwamnatin China mai mulkin gurguzu. Kasar China dai ta zuba hannayen jari na biliyoyin daloli a Najeriya tare da baiwa Najeriyar basussuka masu yawa gwamnatin Najeriya take amfani dasu domin aywatar da ayyukan cigaba cikin gaugawa. Wanda suka shafi manyan ayyuka na habaka sufuri da masana'antu.  Taba wanan rubutu domin bin shfinmu

Kuyi abu uku kacal don yin maganin sauro da maleria ba tare da kun kashe kudade ba.

Image
Sauro mai ramar keta, mugu bakason haske sai duhu. Duk inji bahaushe. Akwai kimanin sauri iri-iri ha guda dubu uku da dari biyar 3500, daga cikinsu akwai iri-iri na macen sauro guda dari hudu da talatin 430. Amma ire-iren macen sauro guda  dari 100 ne ke yada cututtuka. Sauro mugun dabbane mai cutar da dan adam. Haka ta sanya ya kasance abingaba na daya ga al'umar duniya musamman ma Afirka. Sauro ya kasance yana zama sanadiyar mutuwan miliyoyin mutane a duniya a cikin kowasu yan shekaru kadan. A wani rahoto na baya-bayan nan da hukumar lafiya ta duniya ta fitar. Ta bayar da kididdiga game da yawan barna na kisa da cutar maleria keyi sakamakon kamuwa da cutar da mutane a duniya ke yi ta hanyoyi kimanin guda uku. Wanda mafi hadarin su ko yawan kashe al'uma shine cizon sauro. A shekarar dubu biyu da ashirin da daya 2021. Rahoton hukumar lafiya ya bayyana cewa:  Kusan rabin al'umar duniya suna fiskantar barazanar kamuwa da cutar maleria. A wa

Zamu afkawa kasar Nijer da zarar an bamu izinin hakan a cewar General Musa.

Image
Babban hafsan sojojin Nigeria ya bayyana cewa a shirye suke da su afkawa sojojin kasar Nijer da zarar an basu izinin yin hakan. "A shirye muke da mu afka wa sojojin Nijer da zarar an umarce mu da yin hakan. Kuma muna da tabbacin samun nasara. Ba za mu bari masu juyin mulkin su sami nasara ba. Muna da tabbacin masu juyin mulkin da magoya bayansu sun san cewa abinda suke kokarin cin mawa ba mai yuwua bane. Domin zamuyi nasara a kansu" a cewar General Christopha Musa. Kasar Nijer dai tana fuskantar barazanar fadawa cikin yaki tsakaninta da kungiyar ECOWAS wanda kasashe goma zasu shiga tare da tallafin kasar Faransa. Yayin da a daya gefen Nijar zata samu tallafin soji daga kasashen Mali, Burkina Faso da kuma Guinea Conakry masu samun tallafin soji daga kasar Rasha.

zamu yaki kungiyar ECOWAS muddin tayi amfani da karfin soji a Nijer cewar kasahen Mali, Burkina Faso da Guinea Conakry.

Image
Kasashen Burkina faso, Guinea Conakry da jamhuuriyar Mali Sun gargadi kungiyar kasashen Afirka ta yamma ECOWAS cewa bazasu lamunci duk wani matakin soji a kan kasar Nijar ba. Shuwagabanin kasashen na Burkina Faso da Mali da Guinea sun bayyana matsayarsu ne game da hukuncin da kungiyar ECOWAS ta yanke bayan kammala taron ta na gaggawa da ya gudana a ranar 30 ga Yuli, 2023 a Abuja. Game da juyin mulki a Nijar. Matsayar da kasashen uku suka fitar na hadin guwiwa wanda ya samu sa hannun kasashen Burkina Faso da Mali, sune kamar haka: 1. Bayyana goyon bayan al'umar kasashensu na Burkina Faso da Mali da Guinea ga 'yan uwansu na Nijer wadanda suma suka yanke shawarar daukar kawar da mulkin mallaka da ke cigaba da dabaibaye kasarsu, 2. Sun kuma yi Allah wadai da matakin kungiyoyin ECOWAS da UEMOA na yankin Afirka ta yamma a bisa kakaba takunkumi wanda ke kara tsananta wa al'umma da kuma kawo cikas ga karfafa kishin Afirka a yankin na yammacin Afi

Nijar ta dakatar da sayarwa kasar Faransa gwal da makamashin Uranium kuma ta nuna ma Amurka da ECOWAS yatsa.

Image
Sabon shugaban kasa na soji a Nijer  Gen. Abdourahamane Tchiani ya bayyana dakatar da sayarwa kasar Faransa da zinari da kuma makamaahun Uranium.  Hakan na zama martanine bayan kasar Faransar ta dakatar da tallafi da take baiwa kasar ta Nijer. Kaso mai girma na wutar lantarki da ake amfani dashi a Faransa ana samar da shine daga makamahin Uranium. Inda kididdiga ya nuna cewa a kowani daya 1 cikin uku 3 na kwan lantarki a Faransa yana amfani ne da makamashin Uranium da ake samowa daga Nijer. Amma duk da haka kaso 18% ne kacal cikin dari 100% na yan kasar Nijer ke iya ganin wutar lantarki a kasarsu.  Itama kasar Amurka ta sanar da janye tallafi da take baiwa kasar na Nijer. Yayinda sabon Jagoran soji na Nijer Gen. Abdourahamane Tchiani ya mayar da martani da kira ga Amurka da ta rike tallafin nata domin tafi Nijer bukatar su domin tallafawa miliyoyin yan kasar ta da basu da wurin kwana suke rayuwa a titi. Ya kara da cewa duk mai baka riga ka dubi ta wuyarsa. Ya kuma gargadi k

Shahararren mawaki dan kasar Amurka mai hannaye hudu ya bayyana.

Image
Shahraren mawakin gambara na kasar amurka mai suna Daylyt ya wallafa a shafinsa na sada zumunta inda ya nuna hotunansa tare da bayyana cewa maganar boye-boye ta kare yanzu kam zai bayyanawa duniya irin halittar da Allah yamasa. "Allah bai hallici dukkan dan adam dai-dai da juna ba! Yanzu na fahimci dukkan mutane ba daya suke ba. Yanzu na fahimci abinda aka jarabceni da shi alkhari ne ga rayuwa ta! Yanzu kam bana tsoro ko jin kunyar bayyana yadda Allah ya halicceni! Allah yace ma dan adam kazo duniya yadda nayika batare da ka biyani sisin kobo ba! Dalilin haka yasa nima ganinan nazo cikin aminci. Wannan dai bai kasance sabon abu ba domin aduniya Allah ya kanyi halittu iri daban-daban, har da mutanema sukan bambanta a halittar su.