An ceto yara da almajirai ashirin da daya daga chocin ECWA inda aka maidasu kiristoci da karfin tsiya aka kuma tsaresu.
Hukumar tsaro ta farin kaya DSS ta ceto wasu yara da almajirai su ashiri da daya bayan ta kai wani samame a wani gida da ke unguwar JMDB na unguwar Tudun Wada dake garin Jos ta jihar Platue. Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, a ranar 13 ga watan Yuni, wani Abdul Rahman da ya gudu daga gidan ya garzaya zuwa ofishin kungiyar Jammatul Nasril Islam (JNI) don ba da rahoton cewa Cocin ECWA da ke Jos ta satosu su da karfi kuma aka maida su addinin Kiristanci. Ya ce wasu mutane ne suka kama shi da wani Nura Usama da karfi bayan sun sa su aikin wanke musu motarsu a garin Gombe amma suka yi awon gaba da su da karfi a cikin wata mota kirar Toyota Camry, suka kai su Cocin ECWA da ke Tumfure Gombe inda suka shafe makonni uku a tsare, daga nan ne suka yi awon gaba da su. Zuwa hedikwatar ECWA da ke Jos; inda aka tantance su kuma aka kai su wani gida da ke unguwar Tudun Wada inda aka ajiyesu. Kungiyar Jama'tul Nasrul Islam(JNI) ta kai rahoton ga jami’an DSS wadanda sukuma suka kai sama